A matsayinmu na yan kasuwa, ɗaya daga cikin manyan abubuwan da muke tsoro shine rasa duk abin da muka malaka. Gaskiyar ita ce, hakan na iya faruwa a kowane lokaci - tashin gobara, sace sace, ambaliya, hatsari da sauransu.
Inshora yana nan don tabbatar da cewa, lokacin da waɗannan anobar suka faru, ba ku rasa komai ba, kuma a cikin ɗan gajeren lokaci, zaku iya komawa zuwa sana'ar ku.
1. Menene kuka sani game da inshora?
2. Menene tsammanin ku daga inshora?
3. Wadanne irin gogewa kuke dashi game da inshora?
4. Ta yaya inshora ke aiki da gaske?
Idan ba ku sani ba, muna nan don tabbatar da cewa kun san shi, kuma ku amfana daga inshora. Wannan darasi ne mai ban sha'awa kuma mai sauƙi akan Inshora da Takaful. Ku koya kuma ku gudanar da kasuwancin ku cikin kwanciyar hankali.